A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Cibiyar Albasira Qom Karkashin Jagorancin Sheikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) ta isar da sakon ta'aziyyarta na shahadar Ayatullahil Uzma, Shaheed Sayyid Ali Khamenei da sauran Shahidan da suka rasu rayukansu a harin ta'addancin gwamnatin Sahyoniyawa da ɗan ta'adda Trump kan Jamhuriyyar Musulunci ta Iran.
Cikakkiyar sanarwar ita ce kamar haka:
Inna lillahi wa inna ilaihir raji'un!
بسم الله الرحمن الرحيم
من المؤنین رجال صدقوا ما عاهدوا الله علیه فمنهم من قضی نحبه ومنهم من ینتظر ومابدلوا تبدیلا. (احزاب: 23)
Da zuciya mai cike da baƙin ciki da ɗaci, muke nuna alhininmu a gefe guda kuma taya farin ciki na shahadar shugaban musulmi da raunanan duniya, Shaheed Sayyid Ali Khamene'i (R).
Shaheed Ayatullahil Uzma Sayyid Ali Khamene'i (R) ya rayu Shahidi kuma a ƙarshe ya koma ga mahaliccinSa ta maɗaukakiyar hanya (shahada) wadda kowane mumini yake fata da buri. Tabbas da ma irin wannan ƙarshen ne zai zama ladan irin hidimar da kuka yi wa wannan addini da al'umma, koda dai shahada a gaban matsayin ku ba komai ba ce, kamar yadda babban jagora Imam Khumaini (Q) ya faɗa.
Ya Shaheed, muna dada tabbatar muku da cewa wannan tafarkin da kuka tsayu a kai har kuka cimma daɗaɗɗen burin ku, tabbas zamu tabbata a kan sa har mu cimma dayan biyu, nasara ko shahada!
Ga maƙiya kuwa su sani shahada ita ce babban burin kowanne dan makarantar Karbala, ba ta sanya mu mu raunana, sai dai ma tana ƙara mana karfin gwiwa ne da azama, kuma ku sani wannan ta'addancin da kuka yi kun tafka babban kuskure wanda tabbas sai kun girbe shi!
Muna mika sakon ta'aziyyar mu ga Shugaba Baƙiyyatullahil A'azam, Iyalan jagora Shaheed Sayyid Ali Khamenei, Manyan Maraji'ai, Jagora Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H), al'ummar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da dukkanin ƙungiyoyin gwagwarmaya da ma al'ummar duniya, da fatan Allah ya basu hakuri da juriyar wannan babban rashi.
Cibiyar Albasira Qom, Karkashin Jagorancin Sheikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H)
11 ga Ramadan, 1447
Ra'ayinka